5 Afirilu 2021 - 07:54
An Kame Manyan Mutane A Kasar Jordan Bisa Dalilai Na Tsaro

Mahukuntan kasar ta Jordan sun sanar da kame wasu muhimman mutanen kasar da su ka hada da tsohon shugaban ofishin Sarki, bisa dalilai na tsaro.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labarun “ Patra’ na kasar Jordan ya amabci sunan Sharif Hassan Bin Zaid da Ibrahim Awadallah daga cikin wadanda aka kama.

Ita kuwa jaridar “Washington Post” ta bayar da labarin dake cewa; Daga cikin wadanda ake tsare da su a gida da akwai tsohon Yarima mai jiran gado, Hamza Bin Husain, sai dai majiyar gwamnatin kasar ta kore hakan.

Jaridar ta ci gaba da cewa; kame mutanen da aka yi a kasar yana a karkashin wata makarkashiya ce ta kwace mulki daga hannun sarki Abdullah Bin Husain.

Wasu daga cikin wadanda aka kama sun hada jami’an tsaro da shugabannin haulolin Larabawa.

342/